Gwamna Zulum ya bukaci al’ummar Borno su dauki azumi dan neman  afuwar Allah bisa ta’addacin  Boko Haram  

Gwamnan jahar Borno Farfesa Babagana Umar Zulum ya yi kira ga al’ummar jahar da su dauki Azumi a ranar Litinin 24 ga watan Fabrairu domin neman taimakon Allah dangane da bala’in ta’addanci Boko Haram da ya addabesu.

 Zulum ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da ya fitar da kansa a ranar Laraba 19 ga watan Feburairu, inda yace akwai bukatar a hada kokarin da Sojoji da sauran jami’an tsaro suke yi da neman taimakon Allah wajen yakar Boko Haram din.

 Sannan kuma ya bukaci  Shehun Borno da ya  bashi tabbacin umartar dukkanin malamai da limamai dake fadin jahar zasu gudanar da Al-Qunut a duka salloli biyar na ranar Litinin, sannan suma shuwagabannin kiristoci zasu gudanar da nasu addu’o’i na musamman a ranar.

 A  karshe Zulum ya tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na da kyakkyawar niyya wajen yaki da ta’addanci, don haka ya nemi a saka shi a cikin addu’a, Sojoji dake bakin daga da kuma wadanda suka mutu da ma wadanda suka bace da kuma ayanda suka jikkata a dalilin ta’addanci.

 

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More