Gwamnan Bauchi zai tautauna da yan takarar APC da aka kayar

Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar zai zauna da dukkanin ‘yan takarar da suka nemi jam’iyyar ta tsaidu neman kujeru daban-daban da suka kunshi ‘yan majalisun tarayya da jihar domin shawo kan dukkanin korafin da ke akwai.

Gwamnan, wanda ya kuma yaba musu a bisa daukan mataki na hakuri da juriya da suka yi, kama daga wadanda suka ci da wadanda aka kayar.

 

 Gwamnan jihar ta Bauchi ya yi yabo ga ‘yan takarar ne ta cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da Kakakinsa, Malam Ali M. Ali ya aike wa ‘yan jarida a ranar 9/10/2018, inda ya ci gaba da shaida cewar gwamnan yanzu haka yana wani muhimmin aiki a birnin tarayya Abuja, da zarar ya dawo zai nemi dukkanin ‘yan takarar na jam’iyyar APC domin yin ganawa ta musamman da su.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Comment moderation is enabled. Your comment may take some time to appear.