Gwamnan Borno ya zargi sojoji da ‘Karbar Na Goro’

Gwamnan Borno ya zargi sojoji da ‘Karbar Na Goro’

Gwamnan jahar Borno farfesa Umar Babagana Zulum, ya zargi sojoji da karbar na goro wata 1000 daga hannun matafiya.

Gwamnan ya kai ziyarar bazata ne ga wani shingen da sojoji suka kafa da ke kan babbar hanya a garin Jimtilo.

An dai ce gwamna Zulum da kansa ya ba da hannu ga cincirindon motocin da suka yi cirko-cirko a kan titin na Jimtilo, inda mutane suka yi ta yada wa a kafafen sada zumunta.

Rahotunni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin 6 ga watan Janairu 2020.

Sai dai jim kadan bayan kalaman na gwamna Zulum, mai magana da yawun ayyukan rundunar wato  Kanar Aminu Ilyasu ya mayar da martani, inda ya nuna rashin jin dadin rundunar dangane da kalaman na gwamnan.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More