Gwamnan Zamfara Ya Bukaci Sabon Kwamandan Rundunar Soja Kan Tabbatar Da Tsaro

Gwamna jahar Zamfara  Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci sabon Kwamandan rundunar sojoji  ta 8 dake lura da yankin Sakkwato, Mejo Janar Jide Ogunlade da ya ci gaba da bai wa gwamnati goyon bayan wajen tabbatar da zaman lafiya a jahar ta  Zamfara.

Gwamnan ya ji dadin karin girman da Ogunlade ya samu zuwa mukamin GOC inda  yace, an yi masa hakan ne sakamakon nasarorin da ya samu a yaki da yan binciga a Zamfara da kuma matsayinsa na Kwamandan atisayen Hadarin Daji.

Shi dai atisayen Hadarin Daji gamayyar jami’an tsaron Najeriya daban-daban ne suke gudanar da shi wanda hedikwatar sojoji  ke jagoranta domin ganin an kawo karshen hare-haren yan bindigan  jahar Zamfara.

Gwamna Matawalle a wata takarda da Daraktan Gwamnan na  kafafen watsa labarai, Yusuf Idris ya sanyawa hannu ya bayyana cewa ana samun ci gaba a atisayen domin tuni aka rage hare-haren ‘yan bindiga a jahar.

Rundunar sojin ta 8 suke kula da ayyukan sojoji a Jihohin Sakkwato, Kebbi, Katsina da Zamfara.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More