Gwamnati ta kakkarfan shaida aniyarta kafin janye yajin aiki – ASUU

Kungiyar malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU), ta bukaci gwamnatin tarayya da ta nuna shaida kakkarfan aniyarta a kan yarjejeniyar da suka cimma a taron su, kan bukatun su bias  yajin aikin da suke ci gaba da yi.

Shugaban kungiyar Biodun Ogunyemi, ne ya fadi hakan a cikin wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa a Abuja, ranar Litinin, ya ce, kungiyar za ta isar da shawarar da ta zartas a kan tayin da gwamnati ta yi masu a ranar Talata.

Farfesa Ogunyemi ya ce, sabanin abin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa, kungiyar ba ta yi fatali da tayin da gwamnatin tarayya ta yi mata ba, ba ta kuma gabatar da wasu sabbin bukatun ta  ba.

A bayan taron ne, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya ce gwamnati tana gab da warware matsalolin da ke tsakaninta da malaman, wayanda suke yajin aiki tun daga ranar 5 ga watan Nuwamba, 2018.

Ngige ya ce, Ma’aikatar kudi da ofishin babban akawuta  na kasa, sun samar da shaidun biyan Naira bilyan 15.4 na alabashin malaman da aka yanke.

Ya kuma yi nuni da cewa, akwai shaidar tabbacin Shugaban kasa ya amince da biyan bilyan 20 na kudaden ariya na tun 2009 zuwa 2012.

Ngige ya ce, ana kan yin aiki a kan kudaden, da zaran kuma an kammala za a sakewa kungiyar ta ASUU kudaden, gami da sauran bukatun kungiyar. “Muna ta nazartan tayin na gwamnati, mun kammala tuntuban wakilanmu.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More