Gwamnatin APC ta bawa tsohon kwamishinan yansandan Kano makami

Gwamnan jahar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ba bawa tsohon kwamishinan yan sandan jahar Kano wato Mohammed Wakili, wanda yan Kano suka saka masa suna Singham mukami.

Kakakin gwamnan jahar Gombe Ismaila Misilli ya fitar da sanarwa hakan.

Jama’a da dama sun san wakili bisa dalilin jajircewarsa a kan aiki da kuma rashin tsoro, musamman irin rawar da ya taka yayin zaben gwamna aka gudanar jahar Kano na 2019.

Gwamnan jahar Gombe Muhamnadu Inuwa Yahaya, ya amince da nadin tsohon kwamishinan yan sandan jahar Kano a matsayin mai bashi shawara a kan harkokin tsaro tare da fara aiki nan take.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More