Gwamnatin Dubai zata kori mata masu zaman kansa sakamakom mutuwar  wani balarabe

 

Yanzu gwamnatin kasar Dubai ta yanke shawarar kama duk wata mace mai zaman kanta da aka gani a kasar dan mayar dasu kasashen su, sakamakon dalilin mutuwar wani Balarabe da ya kwanta da wata karuwa.

Hukumar yan sanda ta Hadaddiyar Daular Larabawa sun gama shiri tsaf domin tarkato kan karuwai masu zaman kansu a kasar, bayan sun samu gawar wani Balarabe da ya mutu a lokacin da yake zina da wata karuwa a Otel.

Lamari ya faru ne a yankin Hilly Tower Sharjah, wanda  hakan ya sanya aka sanar da yan sanda su kama wasu mata 18 dake yankin da ake tunanin karuwai ne.

A wani bidiyo da aka sanya a shafukan sadarwa, jaridar Information Nigeria ta gano cewa an umarci ‘yan sandan kasar da su tattaro duka mata yan Afirka da suke zaman kansu a kasar dalilin mutuwar Balarabe.

Jaridar legit hausa ta rawaito cewa wani mutum ya wallafa bidiyon yana cewa, Karuwa yar Najeriya ta kwanta da Balarabe ya mutu a lokacin da yake lalata da ita,yanzu gwamnatin Dubai za su dawo da duk wata bakar mace da suka gani tana yawo akan titi.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More