Gwamnatin jahar Borno ta mika bukatun ta 10 ga Buhari

Sarakunan gargajiya, Shugabannin Addini, Kungiyoyin Mata da ‘Yan siyasa, a karkashin jagorancin Gwamnan Jahar Borno, Kashim Shettima, sunyi tawaga zuwa wurin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, dan gabatar masa da bukatun su guda 10, wajen ganin an magance yan ta’addan kungiyar Boko Haram, data addabi  Jahar tasu.

Gwamna Shittima ya ce, bukatun sun samu ne a sakamakon la’akarin da taron da suka yi a kan sha’anin tsaron Jahar a Maiduguri a ranar Litinin ta makon da ya gabata ya haifar.

Duk da cewa, ba a bayyana abin da ke cikin wasikar da suka gabatar masa ba filla-filla, amma dai an ce ta kunshi matakai ne da tawagar take ganin in an yi aiki da su za su taimaka wa kokarin da ake yi na ganin an kawo karshen ‘yan ta’addan na Boko Haram.

tawagar ta kunshi  dattawan, wakilan majalisun Jihar da na tarayya Shuwagabannin kananan hukumomin, Kungiyoyin mata, Kungiyar ‘yan Jaridu da  kuma kungiyoyin kwadago  duk na jahar ta Borno.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More