Gwamnatin Kaduna Na Neman Wabba Da Sauran Jagororin NLC Ruwa A Jallo

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ayyana neman shugaban kungiyar kwadago na kasa (NLC), Kwamared Ayuba Wabba, tare da sauran shugabannin kungiyar ruwa a jallo.

Gwamnatin ta bayyana nemansu ruwa a jallon ne a bisa zargin da ta yi na cewar suna zagon kasa wa tattalin arziki tare da kai hare-hare wa gine-ginen al’umma da suke jihar.

LEADERSHIP ta habarto cewa Mista Wabba ya isa Kaduna ne domin jagorantar mambobin NLC domin gudanar da zanga-zanga tun ranar Litinin bisa adawa da kokarin gwamnati na korar wasu ma’aikatan jihar tare da wasu tsare-tsaren da gwamnatin Nasir E-Rufai ta kawo kan ma’aikatan jihar.

Gwamnan Kaduna ya bayyana cewar duk wanda ya sanar da inda za a samu nasarar cafke Wabba zai samu tukuici mai tsoka.

Gwamna El-Rufai wanda ya ware lokacinsa domin wallafawa a shafinsa na Tuwuta a ranar Talata inda yake ayyana neman shugabanin kungiyar uwa a jallo “Ayuba Wabba da sauran shugabanin NLC na kasa @NLCHeadquaters an ayyana nemansu ruwa a jallo bisa yin zagon kasa wa tattalin arziki tare da kai hare-hare wa kadarorin jama’a a karkashin dokar laifuka iri daban-daban.

“Duk wani da ya san inda ya buya ya aike da sako zuwa ga @MOJKaduna KDSG. Za a baiwa duk wanda ya sanar da inda yake tukuici mai tsoka!”.

Sai dai wakilinmu ya nakalto cewa duk da wannan umarnin, Wabba da sauran shugabanin NLC sun ci gaba da jagorantar zanga-zangar adawa da matakin gwamnatin El-Rufai na korar ma’aikata daga bakin aikinsu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More