Gwamnatin Kebbi zata bada tallafin miliyan 100 ga masu harkar Kifi

Gwamnatin Jahar Kebbi ta bayyana kudurinta na samar da tallafin Naira Miliyan dari ga masu sana’ar kiwon kifi, kamun kifi da kuma ‘yan kasuwar masu sana’ar ta kifi a duk fadin jahar ta kebbi.

Sanarwar ta  fito ne daga bakin Gwamnan jahar, Abubakar Atiku Bagudu a ranar Laraba 7 ga watan 2018  yayin wani taron da gwamnatin jahar ta kebbi ta shirya domin tattaunawa da kungiyoyin masu harkar kifi a cikin fadin jahar ta Kebbi.

Taron tattaunawar ne a dakin gudanar da taro na masaukin shugaban kasa da ke  Birnin-kebbi.

Inda gwamna Bagudu  yace kimanin  dubu biyar daga kananan hukumomi 21 na jahar Kebbi da suka kunshi masarautun Gargajiya guda hudu na jahar, Haka kuma gwamnatinsa za ta gina makurantu na karatu ga ‘ya’yan saboda irin yanayin sana’ar ta masu kamun kifi take”. Ya kuma kara da cewa gwamnatin za ta samar da iraruwan kifi na kiwo wanda za’a sanya a cikin gulaben ruwa fadama a dukkan fadin jahar domin bunkasa harkar kiwon kifi da kuma kasuwar kifi a jahar.

A karshe gwamnatin jahar tace za ta tabbatar da ta samar da babbar kasuwar sayar da kifi a jahar wadda jama’ar kasashen Afirka zasu shigo domin yin kasuwancin sana’ar kifi a jahar”.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Comment moderation is enabled. Your comment may take some time to appear.