Gwamnatin Najeriya  ta bada hutun ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba

Gwamnatin  Najeriya ta fitar da sanarwar ranar  Alhamis 1 ga watan Oktoba 2020 a matsayin ranar hutu, kasancewar  ranar ce  kasar Najeriya ta ciki shekaru 60 da sumun yancin kai.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hutun ne  a madadin gwamnatin tarayya dauke da sa hannun sakataren dindindin na ma’aikatar harkokin cikin gida, Georgina Ekeoma Ehuriah.

Minitan ya taya daukacin al’ummar  Najeriya murnar zagayowar ranar.

Sannan yayi kira ga dukkanin al’ummar  Najeriya dasu hada hannu tare gwamnati mai ci a yanzu wajen tabbatar da tafiyar da ayyukan ta don samar da cigaban waa yan kasa, na nan gida Najeriya  dama na kasashen waje tare da bukasa tattalin arziki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More