Gwamnatin Najeriya ta gargadi ASUU

Gwamnatin Najeriya ta yi gargadi ga kungiyar malaman jami’o’i ASUU da ke yajin aiki inda ministan kwadago ya ce malaman za su ga sakamako idan har suka ki amincewa su koma teburin tattaunawa da gwamnati.

Chris Ngige ya ce gwamnati za ta iya yin aiki da dokokin kwadago da suka dace domin magance lamarin, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ya ruwaito ministan ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Mista Ngige ya ce ya yi wa ASUU tayin tattaunawa ta kafar intanet saboda annobar coronavirus amma kungiyar ta dage cewa sai ta gana da shi keke da keke.

Ministan ya ce kungiyar malaman na yajin aikin ne saboda rashin jituwa da gwamnati kan tsatin biyan albashi IPPIS.

Gwamnati da kungiyar malaman jami’o’in sun sha zama sau da dama, domin tattauna bukatun kungiyar domin kawo karshen yajin aikin da ta dade tana shiga.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More