Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wata hanyar samar wa da yan gudun hijira abinci

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wata hanyar samar da kayayyakin abinci ga ‘yan gudun hijira ta hanyar amfani da jirgi mai saukan angulu, inda za a dinga jefawa ‘yan gudun hijiran abinci daga sama a wuraren da baza a iya kaiwa ta kasa ba sakamakon matsalar tsaro da ake fama da ita.

An kaddamar da shirin ne a filin saukar jiragen sama a birnin Maiduguri.

Ministan ma’aikatar agaji da jinkai ta kasar, Sadiya Umar Farouk ta hallarci wajen kaddamar da shirin.

An sauke wasu daurin abinci daga jirgi mai saukar ungulu ta sama ta hanyar kumbo, wanda ake kira da “Parachute” a turance.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More