Gwamnatin  Najeriya ta zoke batun bude makarantu

Gwamnatin tarayya  ta bayyana cewa,
daliban kasar wadanda suke ajin karshe na sakandire ba za su zana jarabawar WAEC ba, duba da yadda cutar Coronavirus ke cigaba ya yaduwa.

Rahotunnin sun nuna cewa, ministan ilimi na kasar Malam Adamu Adamu ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan taron Majalisar Zartarwa na Tarayya a  birnin Abuja

Inda ya ce har yanzu babu ranar komawa makaranta.

Makarantu zasu cigaba da zama a rufe, har zuwa lokacin da ya kamata a bude,  ya gwammace daliban su zauna shekara daya a gida da ya saka rayuwarsu cikin hadari. Inji ministan ilimi na kasar Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More