
Gwamnatin Najeriya zata bayyana matakan da za a dauka kafin bude makaratun a kasar
Gwamnatin Najeriya ta cewa bada dadewa ba zata bayyana matakan da za a dauka kafin bude makaratun a kasar ta Najeriya
Sakataren gwamnatin Najeriya kuma Shugaban kwamitin kota-kwana na yaki da cutar Covid19 na fadar shugaba Buhari, Boss Mustapha ya bayyana hakan a lokacin da yake hira da manema labarai a birnin Abuja a jiya Laraba.
Inda yace ma’aikatar Ilimi zata bayyana sharuda da matakan da ya kamata a dauka don bude makarantun na kasar Najeriya.