Gwamnatin Nasarawa zata hada kai da kamfanin Dangote dan saraffa amfanin Gona

Rahatonni su nuna cewa,  nan gaba kadan ake sa rai gwamnatin jahar Nasarawa da kamfanin Dangote za su sa hannu a yarjejeniyar gina kamfanin fulawa,  casar shinkafa da kuma noman rogo.

Gwamnan jahar Nasarawa Abdullahi Sule, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kammala shirin aika tawagar jami’an ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu zuwa Legas domin a sa hannu a yarjejeniyar.

Gwamna Sule ya ce a wannan shiri, kamfanin Dangote zai samu katafaren fili har eka 50, 000 domin kafa gona da kamfanin shinkafa a cikin kananan hukumomin Doma da Nasarawa, inda  ya kara da cewa kamfanin fulawa da za a gina a jahar zai ci eka 10, 000 na fili, inda za a rika aikin rogo.

Za a bude wannan katafaren kamfani ne a cikin karamar hukumar Wamba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Kansilolin kananan hukumomi jahar biki daya a gidan gwamnatin jahar tasa, ya kuma  shawarce Kansilolin da ke mulki a jahar da su yi kokarin kawo sababbin dabarun yadda za su samu kudin shiga.

Gwamnan ya ce hakkan zai taimaka masu wajen rike kansu.

“Ina kalubalantar ku da ku nemi hanyar tatso kudi, ku yi wasu ayyuka daban ba biyan albashi ba. Ba zai yiwu mu na kokarin nemo kudi a matsayin jaha, amma duk su kare kan albashi ba”

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More