Gwamnonin Najeriya sun bukaci a wajabta sanya takunkumi yayin fita

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari, da ya amince a wajabtawa jama’a amfani da takunkumin fuska a duk fadin kasar.

Wannan kira ya biyo bayan fargabar da ake da ita na karuwar masu Coronavirus a fadin kasar, kamar yadda gwamnonin suka rubuta a cikin wata wasika.

Gwamnonin 36 na ganin cewa akwai bukatar shugaban kasar ya amince da  bukatar ta su.  Wasikar ta kungiyar gwamnonin ta ce ”yakamata a wajabtawa kowa da kowa amfani da takunkumin fuska kama daga matakin gwamnatin tarayya zuwa na jahohi domin dakile yaduwar cutar ta Covid19.

Har yanzu dai fadar shugaban kasar bata ce komai ba kan  batun, ko Buharin ya samu wasikar sannan ko akwai yiwuwar shugaban kasar ya dauki wannan shawarar.

BBC ta rawaito cewa, wasu majiyoyi biyu daga fadar shugaban kasar sun ce kamar an rubuta wasikar ne da nufin shawara ga kwamitin ko-ta-kwana da shugaban kasar ya kafa.

Sun ce kwamitin zai yi wa shugaban kasar karin bayani a game da shawarar da kungiyar gwamnoni ta bayar a ranar Lahadi.  A bangare guda kuma, kungiyar gwamnonin ta bukaci shugaba Buhari da ya yi gyara a kan dokar hana fitar da ya sanya a jahohin Legas da Ogun da kuma Abuja, babban birnin kasar.

Kungiyar ta ce, yakamata a dan sassauta dokar, sannan kuma a hana zirga-zirga a tsakanin jahohi gami da hana gudanar da taruka.

Kungiyar gwamnoni ta ce idan aka ci gaba da aiwatar da dokar hana fitar, to ya kamata a rinka barin kayayyakin abinci da na kula da lafiya da man fetur da dai makamantansu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More