Gwanatim Kaduna ta bayyana aniyarta na saka hutar lantarki mai amfani da hasken rana a jahar

Gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana shirinta na sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana a wasu gidaje guda 3, 400 na wasu kananan jahohin jahar guda uku, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN. Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnatin ta ware makudan kudi naira biliyan 8.3 domin gudanar da wannan gagarumin aiki a kananan hukumomin Kubau, Jema’a da kuma Kajuru a shekarar 2020.

Shugabar hukumar samar da wutar lantarki na jahar Kaduna Dapola Papoola, ce ta bayyana haka yayin da ta gurfana a gaban majalisar dokokin jahar Kaduna domin ta kare kasafin kudin hukumarta a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba, inda ta ce bayan saka wuta a gidaje 3400, gwamnatin Kaduna ta sanya aikin samar da wutar Solar mai tsawon kilomita 2 a dukkanin mazabun siyasar jahar Kaduna guda 255, a cikin kasafin kudinta na shekarar 2020.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More