Halima Dangote tare da manyan daraktoci 5 sun yi murabus daga kamfanin Dangote

Manyan daraktocin kamfanin Dangote Flour Mills mallakin fitaccen attajiri, Aliko Dangote sun yi murabus daga mukamansu tare da ajiye ayyukansu, dan baiwa wasu damar shigowa suma a dama dasu.

Rahoton jaridar Daily Nigerian tace, shugaban kwamitin gudanarwar kamfanin, Asu Ighodalo tare da wasu manyan daraktocin kamfanin guda 5 ne suka yi murabus, wanda hakan zai bada daman nada wasu sabbin daraktoci guda 4.

Sakatariyar kamfanin, Aisha Isa ta tabbatar da lamarin, inda ta bayyana sunayen sauran daraktocin da suka yi murabus kamar haka, Olakunle Alake, Arnold Ekpe, Yabawa Lawan Wabi, Thabo Mabe, da kuma Halima Dangote.

Kamfanin Dangoten ya maye guraben ma’aikatan da sukayi murabus din a take, Venkataramani Srivathsan, Chandrasekaran Balaji, Mukul Mathur da Anurag Shukla suna daga cikin sabbin ma’aikatan da zasu cigaba da tafiyar da kwamitin gudanarwar kamfanin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More