Hana yan Arewa ganin Buhari ake – Bafarawa

Tsohon gwamnan jahar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya ce yadda tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya fito fili ya rubuta wa Shugaban kasar Muhammadu Buhari wasikar da ta kunshi  matsalar tsaron, hakan ba wani abun aibu ba ne.

A wata hira da BBC tayi da Bafarawa ya ce, Obasanjon ba kowa ya rubuta wa wasikar  ba, bace shugaba  Buhari, inda ya ce matsayin Obasanjo na tsohon shugaban kasa,kuma dan Najeriya, sannan dattijo, yana da damar bayyana fahimtarsa da ra’ayinsa kan halin tsaron da kasar  ta Najeriya ke ciki, sannan kuma ya bayar da shawarwarinsa.

 

Tsohon gwamnan ya ce kamata ya yi Shugaba Buhari ya nazarci wasikar ya duba abubuwan da suke na gaskiya a ciki wadanda kuma ba na gaskiya ba ya yi watsi da su, domin kuwa koda makiyin kane yace “gyara zaman ka ai baya zama sauke mu ra”

A karshe  ya ce  rishin barin a gana da shugaba Buhari yasa wasu manyan kasar ke fitowa fili suna suka ko tsokaci game da wasu abubuwa na gwamnatin  shugaba Buhari,  madadin su  bashi sawara a sirrince ba sai wani yaje ko gani ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More