Hanyoyi guda bakwai na kauracewa cutar Coronavirus da yanzu ta shigo Najeriya

 

  • Kada kaji tsoro
  • Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi (hand gel), da kyau wanda zai iya kashe kwayoyin cuta.
  • Akalla kuyi nisa da mutumin da yake tari ko atishawa na tsawon mita daya da rabi(1.5), ko tsawon takun kafa biyar (5)

 

  • Mai fama da zazzabi kuma yana tari ya zauna a gida ko ya dan kebance daga cikin jama’a kuma kada yayi cudanya da mutane, domin gujewa yaduwar cutar ga wasu.

 

  • Ka tabbatar kai da mutanan dake zagaye da kai kuna kula da tsafta, ta hanyar rufe bakin ku ko hancin ku indan kunyi tari ko atishawa da auduga ko kyalle mai tsafta, kuma ku yarda shi a take- sannan ku wanke hannayenku.

 

  • Zauna a gida idan kana jin alamumin zazzabi, tari,ko fitar nimfashi da kyar (Kadan-kadan)sannan ka gaggauta kiran hukumar hana yaduwar cutuka ta kasar Najeriya wato NCDC ta lambar waya kamar haka 0800-970000-10 a kyauta, wanda ke bude tun daga safiya har zuwa dare. Sannan ku kaurace wa shan magani kanku batare likita ya umarta ba.

 

  • Kuyi kokarin amfanin da ingantattatun kafar yada labaru, hukumar hana yaduwar cutuka ta kasar Najeriya, ma’aikatar kiwon lafiya ta tarayya da kuma ta jahar Legos dan samun labarai da cigaban da ake samu kan lamarin na cutar ta coronavirus.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More