Har yanzu Sarki Sanusi bai wanke kansa ba – Muhuyi Magaji

Hukumar kula da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ba ta gamsu da bayanan da Masarautar Kano ta yi ba kan zargin almubazzaranci da naira biliyan 3.4 da take yi mata ba.

Shugaban Hukumar Muhuyi Magaji ya shaida wa BBC cewa “babu gaskiya a ikirarin masarautar na cewa kudaden da ta gada N1,893,927.38 ne kawai”.

Ya kara da cewa “mun kuma samu shaidun da ke nuna cewa Sarki Sanusi ne ya bayar da umarni ko ya amince da mafi yawan kashe-kashen kudaden da muke zargin an yi ba daidai ba”.

Ita dai masarautar ta musanta wannan zargi da babbar murya, kuma masu goyon bayanta na ganin cewa ana yi mata bita-da-kullin ne kawai saboda dalilai na siyasa.

Dangantaka ta yi matukar tsami tsakanin bangarorin biyu a baya-bayan nan, abin da ya kai ga gwamnati kirkirar sababbin masarautu, lamarin da kuma yake gaban kotu a yanzu haka.

Yayin da bangaren gwamnati ke zargin Sarkin da tsoma baki a harkokin siyasa, a nasu bangaren, magoya bayansa na zargin gwamnati da kokarin cire shi saboda yana fadar gaskiya da kuma marawa talakawa baya.

Jawabin na hukumar yaki da cin hancin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wasu manya suka shiga tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi, lamarin da ake ganin kamar ya kawo karshen takun-sakar da bangarorin biyu ke yi.

Amma Muhuyi Magaji ya sake nanata kiransa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya dakatar da Sarkin domin a samu damar gudanar da bincikenta kamar yadda ya kamata.

Wannan rikici dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a ciki da wajen Kano, kuma ya raba kawunan ‘yan jihar da dama.

An samu tashin hankula a sakamakon lamarin, inda har gwamnati da masarautar suka soke wasu daga cikin bukukuwan sallah saboda dalilai na tsaro.

Masu sharhi na ganin zai yi wuya a kawo karshen lamarin a nan kusa, musamman idan aka yi la’akari da yadda bangarorin biyu ke ja da juna, da kuma yadda ake shari’u da dama a gaban kotu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More