Harin garin Auno na Maiduguri akwai lauje cikin nadi- Kashim Shettima

Tsohon gwamnan jahar Borno, kuma mai wakiltar Borno ta tsakiya a majalisar dattawa sanata Kashim Shettima ya yi kira ga shedikwatar tsaro ta Najeriya da ta gudanar da cikakken bincike game da harin Auno, domin kuwa akwai tambayoyi dake bukatar amsoshi game a harin.

Shettima ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a ranar Talata 11 ga watan Feburairu 2020, inda ya tabbatar da cewar an samu karuwar hare-haren Boko Haram a kwanankin nan a wasu sassan na jahar Borno. Sai dai babu harin daya kai na Auno muni wanda ya auku a daren Lahadi 9 ga watan Fabrairu.

A matsayina na sanata mai wakiltar mazabar Borno ta tsakiya, kuma garin Auno na daga cikin mazabar, ina da daman da zan nemi majalisar dattawa ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike a kan harin da aka kai na garin Auno saboda akwai alamar tambayoyi da dama game da harin da suke bukatar amsoshi.
Nasan adadin Sojojin da suka mika rayuwarsu tare da sadaukar da rayuwarsu wajen kare al’umma jahar Borno, amma na gwammace na yi kira ga shedikwatar tsaro wanda ita ke da hakkin kula da dukkanin ayyukan Sojoji da ta yi gaggawar kafa kwamitin bincike.

“Dole ne kwamitin ya kunshi mutanen kirki masu nagarta, sannan dole ne kwamitin ya nemi wakilai daga gwamnatin jahar Borno, jama’an garin Auno, iyakan mamatan, kungiyoyin direbobi da sauransu.” Inji shi.

Legit ta rawaito cewa a karshe kuma ya nemi kwamitin ta kammala aikinta cikin yan kwanaki kadan, don tabbatar da an yi adalci ga wadanda abin ya shafa tare da kare afkuwar lamarin a nan gaba, musamman ta duba da hanyar da tafi inganci ga matafiya, kuma zata fi sauki kulawa yayin da rikicin ta’addanci, wanda muke fata zai zo karshe nan bada jimawa ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More