Harin yan’bindiga na Sokoto: Shugaba Buhari ya jajantawa mutanen jahar

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya janjanta wa iyalan wadanda suka rasa ransu a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Sabon Birni dake jahar Sokoto. Mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya fitar da sanarwa cewa, shugaba Buhari ya yi addu’ar samun sauki ga wadanda suka samu raunuka.

Shugaban ya bayyana cewa abin takaici ne a ce ‘yan bindiga suna kai hare-hare a irin wannan lokaci da duniya da Najeriya ke fama da tsanani na wannan annobar ta Covid19.

Sannan kuma ya yi alkawarin cewa rundunar da aka kaddamar domin yakar masu tayar da kayar baya a arewa maso yammacin Najeriya za ta ci gaba da yakar ‘yan bindigar da suka addabi yankunan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More