HDP Ta Bukaci Kotu Ta Dakatar Da Rantsar Da Shugaba Buhari

Jami’iyar HDP wato Hope Democratic Party, a Najeriyar ta shigar da wata kara inda take  neman Kotun zaben shugaban kasa ta dakatar da rantsar da Shugaban Mohammadu Buhari,  wanda yake gabatowa a nan kusa, cewar ana kalubalantar nasarar da ya yi a kotu.

A wata rubutaciyar takardar jawabi da Jamiyar HDP ta raba wa manema labarai na nuni da cewa sun shigar da karar ne a bisa wasu dalilai da dama, amma muhinmi dalili shi ne cewa akwai wata shari’a da aka riga aka shigar dake kalubalantar nasarar da shugaba Mohammadu Buhari ya samu a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu 2019

Kwararre a bitar kundin tsarin mulki, Barista Mainasara Kogo Ibrahim ya yi fashin baki a kan ko Jamiyar ta HDP na da hurumin shigar da karar

Inda yace duk da an kammala shirye-shiryen rantsar da shugaban kasar, jamiyyar na da hurumin  shigar da kara amma kuma matakin hakan na iya harfar da rudani.

A jawabin  tsohon shugaban hukumar wayar da kan al’umma ta kasa, Dokta Mike Omeri ya ce duka da cewa Jamiyar Jamiyar HDP tana da hurumin shigar da kara amma a yi taka tsantsan saboda duk abin da kotu zata yi, a bi abin da dokar kasa ta tanada domin kada a jefa kasa a cikin wani halin kakanakayi.

Jamiyar Jamiyar HDP ta ce an riga an kaiwa shugaba Buhari takardar karan dake bayanin cewa in har an dasa ayar tambaya a wajen Kalubalantar zaben nasa, toh bai cancanci daukar rantsuwa ba

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More