Hukumar INEC zata rufe karbar katin zabe 9 ga watan Fabrairu

Hukumar zabe mai zaman kanta wato  INEC ta ce zata fara raba katin zabe na dindindin wato PVC a cibiyoyin da akayi rajista a fadin kasar nan, daga ranar 16 ga watan Junairun .

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da kwamishinan zabe na kasa, kuma shugaban kwamitin, wayar da kan al’umma kan harkokin zabe, Mista Festus Okoye a Abuja.

Mista Festus ya ce ranar 8 ga Fabrairu itace ranar karshe da hukumar zata raba katin zaben.

Sanarwar ta bayyana cewa, an yanke wannan shawara ne a taron mako-mako da ake gudanarwa na ranar Alhamis a Abuja.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More