Hukumar Kwastam ta kama $8m a filin jirgin sama na jahar Legos

Hukumar yaki da fasa kauri ta kasar Najeriya (Kwastam) ta kama $8,065,615 a filin jirgin saman na Murtala Muhammed dake  jahar Legas.

Shugaban hukumar Hameed Ali, ya sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a garin  Abuja Talata,inda yace, an kama makuden kudaden ne a wata mota a filin jirgin yayin da ake yunkurin zuba su a jirgin saman.

 

Sai  dai ba’a  bayyana jirgin ba, amma an bayyana cewa motar da aka kama kudin a ciki, wanda mallakar Nigerian Aviation Handling Company (NAHCO).

Ali ya ce wanda ake zargin matukin motar ne kuma ma’aikacin NAHCO.

An kama shi ne sakamakon zargin da ake masa na almundahanar kudade, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Ya ce an nade makuden kudaden ne a ambulan mai ruwan kasa tare da sunayen wadanda za a ba kudin.

“Daga rana da muka kwace kudaden, babu bankin da suka fito suka ce nasu ne.

Amma kuma bincikenmu zai bankado mamallakan kudin,” inji Ali

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More