Hukumar Kwastam Ta Kama Tabar Wiwi cikin akwatin Gawa

Hukumar hana fasa kwauri ta kasar Najeriya, ta bankado wata damara da masu fasa kwaurin tabar wiwi keyi na shigowa da ita cikin Najeriya daga kasashe makwabtan.

Sakamakon wannan mataki dai hukumar ta kwastam ta kama wani akwatin gawa da aka sanyawa sunkin tabar wiwi har 55 .

Kwanturola Mohammed Uba Garba, shine kwanturolan kwastam mai kula da kan iyakan Najeriya da jamhuriyar Benin, da ake kira Seme Border. Yayi karin haske game da wannan kamun, inda yace jami’an su sun kama akwatin gawa da aka sanya sunki 55 na tabar wiwi, kuma har gawar sai da suka bude domin tabbatar da cewar ba’a sanya tabar a cikin ta ba.

Wannnan wata sabuwar dabara ce da muka gano, kuma zamu ci gaba da saka ido domin magance haka anan gaba.

Bayan tabar wiwi da hukumar ta kama har ila yau, wasu kayan da aka hana shigowa dasu Najeriya da suka hada da shinkafa da motoci, inji kwanturola Uba.

Kwanturola Uba Garba ya kara da cewa ina kira ga ‘yan Najeriya musanmman wadanda ke zaune akan iyakan Najeriya, da su ci gaba da taimaka mana, domin ta haka ne za’a kawo karshen zagon kasa ga tattalin arziki da ‘yan fasa kwauri keyi.

A makon jiya ne dai hukumar ta kwastam tace, yana iya yiwuwar sake bada izinin shigowa da motoci ta kan iyakan Najeriya da kasashe makwabta, a cewar kwanturolan hukumar kwastam mai magana da yawunta Mr Benjamin Aber, da zarar an cimma matsaya da hukumar kwastam ta kasar Benin.

A bangare daya kuwa, masu saida motoci sun nuna jin dadinsu akan hakan, hakan zai taimaka wajen farfado da ayyukan yi, domin matakin farko da aka dauka ya sanya manbobin su cikin wani hali na kaka nikayi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More