Hukunci kisa kotu ta yanke wa Maryam Sanda

Maryam Sanda cikin tashin hankali yayin da wata babbar kotun dake babban birnin tarayya Abuja ta yanke hukunci kisa a kanta Mai shari’a Yusuf Haliluya, ya zartar da hukuncin kisa a kan Maryam Sanda, wacce ake zargi da kashe mijinta a shekarar 2017, ta hanyar rataya.

An soma zargin ta ne tun a Nuwamban 2017 da laifuka biyu da suka hada da kashe mijin nata mai suna Bilyaminu Bello, wanda dane ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa Haliru Bello,Inda aka gurfanar da Maryam Sanda a kotu bisa zargin kisan mijinta a watan Disamban 207 Alkalin ya ce an samu dukkanin wasu shaidu da suka tabbatar da cewa Maryam ce ta aikata wannan laifi, inda yayi watsi da ikirarinta na cewa mijin nata ya fadi ne kan fasasshiyar tukunyar Shisha, yayi sanidiyyar mutuwar tasa.

Kotun ta gamsu da hujjojin da aka gabatar na cewa Maryan ta caka wa mijin nata wuka ne yayin da rigima ta kaure a tsakaninsu.

A lokacin da alkali ya zartar da hukuncin wadda ake tuhuma ta yi kokarin rugawa domin guduwa daga zauren kotun sai dai jami’an tsaro sun rike ta.

Jami’an tsaro sun riko wacce ake tuhumar lokacin da taiy yunkurin arcewa daga zauren kotun bayan da alkalin ya yanke hukuncin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More