Ina goyon bayan gwamnatin PDP a Zamfara – Abdulaziz Yari

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Sakamakon soke zabukan  Jahar Zamfara kotun koli ta yi karkshin jam’iyyar APC, alamu sun nuna cewa  Gwamna jahar Zamfara Abdul’aziz Abubakar Yari ya saduda.

Inda yake  bayyana cewa, za su mara wa gwamnatin jam’iyyar PDP baya, don ganin an samu zaman lafiya da cigaban jahar.

Gwamna Yari ya bayyana haka ne jim  kadan da kammala tattaunawa da dattawan jam’iyyar APC da ‘yan majalisar dokokin jahar da na zartarwarsa a gidan gwamnati da ke Gusau dake  babban birnin Zamfara.

Gwamnan ya bayyana cewa, “duk da kokarin da mu ka yi na ganin an yi amfani da zaben fidda gwani na zaben da ya gabata abu ya ci tura. 

Mun dauki kaddara, haka Allah ya hukunta kuma shi ne mafi alheri a gare mu, kuma duk goyan baya da gudunmuwa da ya kamata mu ba wa wannan gwamnatin, za mu yi iyaka kokarinmu wajen bai wa gwamnatin jam’iyyar PDP na samun nasara da cigaban jaharmu da kasa bakidaya. Gwamna Yari ya kuma tabbatar da cewa, siyasa yanzu su ka fara. Kuma sunanan cikin  a jam’iyyar APC; babu gudu, ba ja da baya,” in ji shi.

A karshe gwamna Yari yace basu yi zargi kowa bisa al’amarin da ya faru ba, sun dauka kaddarar Allah ce, tara da yin kira ga dukkan magoya bayan sa yan jam’iyyar APC da su mara wa sabuwar gwamnati baya,

gurin ganin ta kawo cigaba ga jahar tare da kasa baki daya, inda ya mika godiya  ga al’ummar jahar Zamfara dasu ka bashi goyon baya na tafiyar da mulkinsa har tsawon shekaru 8, wanda yanzu canji ya wakana kuma ba dan jam’iyyar sa ba.

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More