Ina kudaden da aka kwato? mai aka yi da su? : Sarkin Musulmi ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi bayani

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III a ranar Talata ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta bayyana wa ’yan Najeriya yawan adadin kudade da kadarorin da ta kwato daga hannun wadanda suka sace da inda aka yi amfani da su.
Ya bukaci hakan ne a Sakkwato a wurin tattaunawar shiyyar tare da masu ruwa da tsaki kan Manufofin da’a na Kasa, wanda Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya shirya, tare da hadin gwiwar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka masu alaka na shiyyar arewa maso yamma.
Sultan din, wanda Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya wakilta, ya ce yin shiru a kan dukiyar da aka kwato zai kawo cikas kan yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
“Yan Najeriya na bin Gwamnati bashin bayani , muna so mu san yadda aka kwato biliyoyin nairori daga shugabanninmu na baya. Ina kudaden suke kuma me sukeyi dasu?
“Wannan bayanin ya zama dole idan aka yi la’akari da yanayin iliminmu da sauran abubuwan more rayuwa kamar hanyoyi wadanda suke bukatar kulawa ta musamman daga gwamnati,” in ji shi.
Ya ce wadanda suka kafa Khalifanci na Sakkwato sun rubuta litattafai da yawa kan cin hanci da rashawa da kuma yadda za a magance su ta amfani da hanyoyin Musulunci.
Sarkin Musulmin ya bukaci shugabannin Najeriya da su samo kwafin wadannan littattafan domin a shiryar da su wajen magance cin hanci da rashawa.
Shugaban shiyyar na hukumar ICPC da ke kula da jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara, Ibrahim Alkali ya ce tsarin da’a da tabbatar da yin gaskiya na kasa ya zama dole domin kuwa “an kirkire shi ne kuma an fitar da shi ne daga mawuyacin halin da ake ciki na sake farfadowa da sabunta dabi’unmu na gaskiya a matsayin kasa. ”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More