Ina murnar dawowar  ka jam’iyyar mu ta PDP:  Atiku ga Gwamna Obaseki

Gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Gwamna Obaseki ya bayyana shiga jam’iyyar ta PDP ne ranar Juma’a da rana a sakatariyar jam’iyyar da ke Benin, babban birnin jahar, kamar yadda PDP ta wallafa a shafinta na Twitter.

 Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugabancin kasar a jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya yi maraba da gwamnan  Obaseki.

Atiku ya wallafa sakon taya munar ne a shafinsa  na Twitter kan shigar gwamnan jam’iyyar tasa ta PDP, inda ya kara da cewa,  “PDP ita ce hakikanin jam’iyya ga  al’umma”.

“Ka shigo jam’iyyar PDP ne lokacin da aka sauya fasalinta ta yadda take son aiwatar da mulki na gari domin  ‘yan kasar Najeriya su amfana,” in ji Atiku Abubakar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More