Ina son zama shugaban majalisar wakilai – Gudaji Kazaure

Dan majalisar wakilan Najeriyar nan mai yawan raha da barkwanci Honorabul Gudaji Kazaure ya ce babban burinsa bayan zabukan 2019 shi ne ya zama shugaban majalisar.
Honorabul Gudaji Kazaure ya sake lashe zaben mazabarsa ta Kazaure da Yankwashi da Roni da kuma Gwiwa a wadannan zaben 2019.
A wata hira da ya yi da BBC, Kazaure ya ce bai taba ganin zaben da ya burge shi wanda aka yi cikin tsari da kwanciyar hankali ba irin na 2019.
“Mutane sun fito sun zabi abin da suke so kuma sun nuna wa duniya cewa Najeriya kasa ce da ta san ‘yancin kanta, domin ‘yan Najeriya sun yarda da wakilcinmu shi ya sa suka kada wa jam’iyyarmu kuri’a,” in ji shi.

Kazaure ya ce bai kamata jam’iyyar adawa ta PDP ma ta dinga zargin an yi magudin zabe ba, don kuwa “kowa ya shaida an yi sahihin zabe.”
Ya kuma mika godiyarsa ga al’ummar mazabarsa tare da yi musu alkawarin cewa zai sake jajircewa wajen tabbatar da yi musu wakilci nagari.
“Sannan ina son zama Kakakin Majalisa, idan har Allah ya ba ni shi ke nan.
“Idan har Allah ya sa na zama shugaban majalisa to kawai duk abin da shugaban kasa ya aiko ta gabana, daga guduma kawai zan yi na buga, shi ke nan ya wuce,” a cewarsa Ina son zama shugaban majalissar wakilai ta Nigeria’ ‘
Kazaure ya ce hakan ba zai zama wata matsala ba, ko bai wa bangaren shugaban kasa damar cin kare ba babbaka, domin ya san duk abin da shugaban kasar zai aiki to, mai kyau ne.”
“Ba mai kalubalantar hakan domin ‘yan APC ne mafi yawa a majalisar. In dai na zama kakaki duk kudurin da shugaban kasa ya aiko, kawai cewa zan yi a madadin sauran ‘yan majalisa zan buge shi da guduma kwam, sai ya wuce.”
Daga nan, ya bukaci jam’iyyar adawa da cewa kada su ce za su ki karbar sakamakon zaben don kuwa “allura ce za ta tono garma.”
Wannan ne dai karo na biyu da Honorabul Kazaure, mai shekara 47 ya ci zabe a matsayin dan majalisar wakilan Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More