INEC na siyar wa APC katin zabe – Atiku

Tsohon Mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’yyar PDP, Atiku Abubakar, ya zargi hukumar zabe  wato INEC,  cewar tana sayarwa gwamnonin jam’iyyar APC katin zabe don a shirya magudi da su a  zaben mai gabatowa na 2019.

Atiku  ya bayyana hakan ne   wajen yakin neman zaben sa da ya hallarta a garin Osogbo dake jahar Osun, da aka gudanar a Nelson Mandela Freedom Park, na garin Osogbo.

Tun da farko dai, Atiku, ya ziyarci basaraken Owa na Obokun Ileshaland, Oba Gabriel Aromolaran da kuma Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, a fadarsu inda ya ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kasa cika dukkan alkawurran da ya yi kafin yakin neman zaben 2015 kuma bai kamata a sake zabensa ba a zabe mai gabatowa na 2019.

 

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More