INEC ta gabatar da Takardar Shaida Ga Obaseki

INEC ta gabatar da satifiket din ga Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu

Obaseki shine ya lashe zaben takarar gwamnan jahar Edo, ya samu kuri’u 307,955 a fadin kananan hukumomin 18 na jihar don kayar da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Osagie Ize-Iyamu, wanda ya samu kuri’u 223,619.

APC ta amince da shan kaye a zaben sannan ta taya Obaseki murna.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana sakamakon zaben a matsayin wata nasara ga dimokiradiyya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More