Iyayen yara sun ki zuwa su dauke yayansu dake gidan mari dake Kano

Iyayen yaran da suka kai ‘ya’yansu gidajen mari a jihar Kano a arewacin Najeriya domin gyara tarbiya sun ki zuwa daukarsu duk da umurnin gwamnati na rufe gidajen.

Gwamnatin Kano ta bayar da umarnin rufe gidajen marin da ake tsare ‘kangararru’ a fadin jahar, tare da ba iyayen yaran wa’adin kwana uku su dauke ‘ya’yansu, a  ranar Litinin.

An rufe gidajen marin ne saboda yadda ake cin zarafi da take hakkin dan adam da ake zargin ana yi a gidajen marin.

Amma har yanzu iyayen yaran sun ki zuwa daukar ‘ya’yan nasu.

BBC ta kai ziyara wasu daga cikin gidajen marin da aka bayar da umurnin rufe su amma masu gidajen marin sun bayyana damuwa game da rashin bayyanar iyayen yaran da aka kawo musu.

Malam Ibrahim Sharifai shugaban kungiyar masu gidajen Mari a Kano ya shaida wa BBC cewa sun sanar da iyayen yaran da aka kawo masu domin gyara tarbiya kan umurnin na gwamnati.

“mun kira wayoyin iyayen yaran amma suna fargaba kan abin da za su iya fuskanta bayan dawowar yaran,” in ji shi.

Ya kara da cewa matakin na gwamnatin ya jefa su cikin tsaka mai wuya saboda yadda iyayen suka ki waiwayar ‘ya’yansu da kuma daliban da suka ce ba zu koma gida ba saboda karatun addini da suke.

Shi ma Malam Mamman mai makarantar gidan mari a Kano, ya ce sun kira iyayen amma sun ki zuwa daukar ‘ya’yansu.

Ana ganin dai wannan wani kalubale ne ga gwamnati saboda yadda iyayen yaran suka ki zuwa daukar ‘ya’yansu da kuma wasu daliban da suka ce za su ci gaba da zama a gidajen marin.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More