Jahahi  21 ne a Najeriya Coronavirus ta bulla ciki

Hukumar takaita yaduwar cututtuka ta Najeriya ta tabbatar da bullar Coronavirus  a jahohin kasar 21 har da babban birnin Abuja inda zuwa yanzu mutum 627 suka harbu.

Hukumar ta NCDC ta bayyana  hakkan ne a shafinta na tiwita cewa an samu karin mutum 86 da suka kamu da cutar ranar Litinin 20 ga watan Afrilu 2020 a  kasar ta Najeriy

Sabbin mutane sune:

70 a jahar Legos
7 a birnin tarayyar Abuja
3 a jahar Katsina
3 a jahar Akwa Ibom
1 a jahar Jigawa
1 a jahar Bauchi
1 a jahar Borno

Daga misalin 11:50 na daren Lahadi an samu adadin mutane 627 masu dauke da Coronavirusa Najeriya.

Karon farko ke nan da aka samu bullar  annoba a jahohin Jigawa da Borno.

Ana jin wadannan ne alkaluma mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar korona rana daya a Najeriya da hukumar ta fitar tun bayan fara samun annobar ranar Alhamis 27 ga watan Fabrairu.

 Sannan kuma hukumar ta ce adadin masu cutar yanzu a Kano 36, bayan mayar da wani mutumin jahar Jigawa da ya kamu da cutar zuwa mahaifarsa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More