Jamiyyun adawa zasu hada kai wajen tsayar da dan takarar shugaban kasa dan kada APC a 2023

Shin kuna ganin zasu zamu nasara?

Tsohon shugaban majalisar jam’iyyun Najeriya na IPAC, Dr. Yunusa Tanko, ya bayyana cewa wasu jam’iyyun adawa za su hada-kai su fitar da dan takara guda domin su nemi mulki a zaben 2023.

Dakta Yunusa Tanko ya taba takarar shugabancin kasar Najeriya.

Tanko yace zasu yi hakan ne domin gwada sa’a su ta yin takarara shugaban kasa a 2023.

Jaridar legit ta rawaito cewa shugaban jam’iyyar NCP yace,yan Najeriya za su so su ga an fito da yan takarar da za su iya doke jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a babban zaben.

Tanko ya bayyanawa ma nema labarai hakan wajen bikin da jam’iyyar NCP ta shirya na cika shekaru 25 da kafata. Inda suka gudanar da bikin a ranar Talata 1 ga watan oktoba 2019 wato ranar da Najeriya ta samu yancin kai.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More