Jarin Abubawan da ake zargin Sowore dashi

Wata Majiya ta bayyana cewa jami’an tsaro sun yi wa Omoyele Sowore wanda ya ke a garkame tambayoyi game da zargin alakarsa da ‘Yan ta’addan Boko Haram da wasu kungiyoyi.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa zargin hannu a cikin tafiyar Boko Haram ya na cikin sababbin zargin da ake jifan Sowore da su.

Kamar yadda kuka sani an sake damke Sowore, yayin da Jami’an tsaro ke tambayarsa game da alakarsa da Boko Haram, kungiyar Shi’ar Najeriya ta IMN da kuma kungiyar IPOB mai fafutukar neman yancin kasar wato Biyafara.

Irin tambayoyi ne aka yi wa Sowore a Ranar 12 ga watan Nuwamba 2019. Sai dai lauyoyin nasa sun bayyana cewa, ina bibiyar sa da zargin hakan ne domin samun hanyar cigaba da tsare sa.

Rahotannin na nuna cewa Sowore ya na ta cigaba da nuna cewa bai da alaka da kungiyoyin. An samu wannan bayani ne kwanaki kusan goma da jami’an DSS su ka sake damke shi.
Tambayoyin da jami’an tsaron su ke yi wa tsohon ‘Dan takarar shugaban kasar ya nuna cewa akwai yiwuwar a gabatar da shi a kotu gaban Alkali bisa zargin hannu wajen aikin ta’addanci.

Inibehe Effiong, wanda ya na cikin Lauyoyin da ke kare Sowore a kotu ya bayyana cewa ba yanzu aka fara kokarin jifarsa da zargi hakkan ba, a baya an bincikesa a kan haka, kuma ba’a samu komai ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More