Jarumin Bollywood Sushant Singh Rajput ya kashe kansa

BBC ta rawaito cewa, yan sanda a Indiya sun ce sun iske ɗaya daga cikin fitattun jaruman Bollywood Sushant Singh Rajput a gidansa da ke Mumbai

Suna tunanin jarumin mai shekara 34 ya kashe kansa ne wanda aka ruwaito kafin mutuwarsa cewa yana fama da da matsalar damuwa.

Ya fito a fina-finai kamar Kai Po Che and M.S Dhoni — tarihin ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan kuriket a Indiya.

A kwanakin da suka gaba ne kuma aka isko gawar manajan jarumin Disha Salian a mace.

Abokan sana’arsa da kuma masoyansa da dama ne suka yi jimamin rashinsa a Twitter tare da yin ta’aziyya ga iyalinsa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More