Kada ku sassautawa yan ta’adda – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci rundunar sojojin Najeriya da su tabbatar da dawo da cikkaken zaman lafiya a kasar baki daya, musamman a yankuna da jahohin da yan ta’adda suka yi katutu a cikin ta, sannan yace kada ko wannan su ya sa ya sassauta wa yan ta’addan.
 
Umarnin ya bayyana ne a ranar Asabar 17 ga watan Agusta 2019 a garin Katsina yayin sa shugaba Buhari ke kan hanyarsa ta dawo wa Abuja bayan ya yi hutun Sallah a garin Daura, ya ce, “Kada ku sassauta wa yan ta’adda ta ko wanne fanni’’.
 
Sanarwar ta fito ta bakin mai ba shugaban kasar shawara a fannin watsa labarai, Malam Garba Shehu a takardar da ya sa wa hannu a ranar Asabar 17 ga watan Agusta a babban birnin tarayyar Abuja, inda yace umarnin ya zama ya zama wajibi ne saboda a halin yanzu yan ta’adda na cin karensu ba babbaka ta hanyar kisa al’umma da kwace dukiyarsu ba tare da tausayawa ba.
 
Garba Shehu ya kara da cewa, shugaban kasar ya jaddada wa dakaru da hafsoshi 175 na rundunar ta 17 na ‘Army Brigade’ da kuma dakarun rundunar sojojin sama na ‘213 Operational Base’ dake Katsina, wadanda ke cikin shirin nan na “Operation Hadarin Daji’’, a filin tashi da saukar jiragen sama na Umaru Musa Yar’Adua dake jahar ta Katsina.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More