Kada ku zabi gwamnoni da ba zasu iya biyan ku albashi ba – Buhari

Shugaban Kasar Najeriya  Muhammadu Buhari ya gargadi talakawan Najeriya kan zaben  gwamnonin da basu  yi  amana  da ayyukan ba  a tsawon mulkin su musamman irin wadanda suka kasa biyan su albashi da sauran hakkokin su.

Shugaba Buhari yace babu wani  dalilin da zai hana  gwamnoni biyan albashin ma’aikatan jihohin su ba, domin gwamnatin tarayya ta ba wa gwamnoni kudi dan gudanar da ayyukan da yake wuyan su.

Buhari yace yana mamakin yadda irin wadannan gwamnoni kan iya kwantawa har su yi barci bayan sun san akwai mutanen dake aikin gwamnati basu biya su albashin su ba, sanin suna da gidaje, suna da iyali, kudin haya , bukatun iyalansu , da suka hada da biyan kudin makaranta, da zuwa asibiti da sayen abinci da dai sauran su.

Shugaba Buhari yace tsarin dokar Najeriya ya ba gwamnonin ‘yancin kashe kudaden da suka samu ba tare da tsangwama ba, sai dai wannan ya zama damar da wadansu suke fakewa suna kin yi wa talakawa aiki.

A dalilin haka Buhari ya shawarci talakawa su yi amfani da ‘yancin su na zabe su zabi wadanda suka chanchanta ,da kuma wayanda suka sana sa zu iya yi musa aiki.

Kamar yadda sashen Hausa na VOA suka ruwaito, da aka tambayi shugaba Buhari game da batun yaki da cin hanci da rashawa, shugaba Buhari yace hanyar da yake bi a halin yanzu ita ce hanyar da tsarin dimokradiya ya amince da shi.

Yace a baya ya dauki wani matakai  dabam, amma kasancewa yanzu ana mulkin dimokradiyya ne tilas yabi tsarin. Sai dai yace duba da cewa tsarin na  daukar lokaci, duk da haka, ana samun nasarorin gaske a abin da a kasa a gaba.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More