Kada Sallar Idi ta wuce awa daya a Abuja – FCTA

An bai wa Musulmi mazauna birnin Abuja karfe 8:00 zuwa 10:00 na safe a matsayin lokacin da za su gudanar da Sallar Idi, kamar yadda wata sanarwa da hukumar FCTA karkashin ministan birnin  na Abuja ta fitar.

Sannan kuma kada sallar ta wuce tsawon sa’a daya.

Umarni na daya daga cikin sharudan da hukumar Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja (FCTA) ta bayar na gudanar da sallar a yunkurinta na kau da  yaduwar cutar ta Covid19.

Kazalika ba za a gudanar da sallar a filin idin Abuja na National Eid Prayer Ground da ke kan Titin Umaru Musa Yar Adua ba.

“An umarci mutane da su gudanar da sallolin a masallatan Juma’ar unguwanninsu,” a cewar sanarwar.

“Dukkanin bukukuwan Idi za a yi su a cikin gidaje sakamakon dokokin da aka saka na rufe wuraren shakatawa da wasanni da nisshadi suna nan daram.”

Kafa sharudan sun biyo bayan wani taro ne da Minista Muhammad Bello ya yi tare da majalisar malaman Abuja ta Abuja League of Imams Initiative ranar Litinin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More