Ka’idoji nabi kafin siyan bindigu kirar AK47 – Amosun

Tsohon gwamnan jahar Ogun Ibikunle Amosun, ya bayyana cewa  gwamnatinsa ka’ida ta bi wajen  siyan  bindigogi kirar AK47 da alburusai har guda miliyan hudu da motocin sulke na yaki kirar APC da rigunan da huluna da harsashi baya ratsa su da wasu kayan sadarwa na tsaro.

A wata sanarwa da kakakinsa, Rotimi Durojaiye ya fitar, Amosun ya ce gwamnatinsa ta samu izini daga ofishin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro na tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan,ya bayyana cewa gwamnatinsa ta bayar da kudade masu yawa wurin sayo makamai a 2012 domin yaki da kallubalen tsaro da suka adabi jahar a wancan lokacin.

Ya ce sauran makaman ne ya mika wa kwamishinan ‘yan sanda a ranar 28 ga watan Mayu amma ya ce babu ko da bindiga kirar AK 47 guda daya cikin makaman da ya mika wa kwamishinan.

Amosun ya kuma ce gwamnan jahar mai ci a yanzu, Dapo Abiodun a wancan lokacin shine babban wanda aka bawa kwangilar sayo kayayakin tsaro ciki har da motoccin sulke wanda ya mika wa ‘yan sanda a karshen wa’addinsa.

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More