Kalaman Trump  yasa Majalisar Amurka na tunanin tsige shi daga karagar mulki

Shugaban wani kwamiti mai karfin iko a Majalisar Dokokin Amurka ya ce kalaman da Shugaban Kasar Donald Trump ya yi a tattaunar da ya yi ta tarho da Shugaban Ukraine na iya bayar da damar a tsige shi daga kan karagar mukaminsa.

wanda shi ne Shugaban kwamitin sa ido kan bayanan Sirri da tsaron ta kasar Amurka Adam Schiff, ya matsa wa fadar White House kan ta  saki cikakkun tattaunawar.

Rahotanni daga Amurka na cewa Shugaba Donald Trump ya matsa wa Shugaban Ukraine Bolodmir Zelenski ya sake gudanar da bincike kan dan Joe Biden,wato Hunter Biden wanda shi ke kan gaba wajen neman zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Democrat.

Mista Schiff, ya ce idan ta tabbata Mista Trump na kokarin tursasa wa Shugaban wata kasa ya ba shi bayanan sirri kan wani abokin hamayyarsa a siyasa, to babu makawa sakamakon laifin da ya aikata zai kasance a iya tsige shi daga kan mukaminsa.

Mista Trump ba musanta zargin hakan ba inda ya amince kan cewa ya tattauna batun kuma ya ambaci sunan Joe Biden a yayin tattaunawarsu. Amma Trump yace yana da yancin yin haka.

Sai dai zuwa yanzu babu wani bayanin daya fito daga fadar White House kan a’lamarin

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More