Kamaru ta dawo da ‘yan gudun hijirar Najeriya 5,000 zuwa Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa an dawo da ‘yan gudun hijirar Najeriya dubu 5 zuwa jihar daga Kamaru.
A cewar wata sanarwa a shafin Facebook na Zulum, musayar yan gudun hijirar ya gudana ne a ranar Litinin kuma ya samu jagorancin Ministan Ministan Yankin Kamaru, Paul Atanga Nji, da wasu jami’an kasarsa.
Wadanda suka dawo din suna daga cikin dubun- dubatar ‘yan Najeriya, akasarinsu daga Borno, wadanda tun a shekarar 2014, suka tsere cikin rukuni zuwa sansanin Minawao da ke Mokolo,
yankin arewa mai nisa na Kamaru, don gujewa kashe-kashen Boko Haram.
Sanarwar ta ce, “Jami’an Kamaru, karkashin jagKungiya Ministan kula da Yankin, Paul Atanga Nji ta dawo da kuma mika rukunin farko na yan gudun hijirar Najeriya 5, 000 ga Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.
“An yi musayar ne a ranar Litinin, a wani takaitaccen biki a Amchiide, wani yankin kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru, kusa da Banki a karamar hukumar Bama da ke tsakiyar Borno.
“Wadanda suka dawo din suna daga cikin dubun-dubatar yan Nijeriya, galibi daga Barno, wadanda tun a shekarar 2014, suka gudu cikin rukuni zuwa sansanin Minawao da ke Mokolo, yankin arewa mai nisa na Kamaru, don gujewa
kashe-kashen Boko Haram.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More