Karin farashin man fetur da wutar lantarki: Dalilin yasa Kungiyar Kwadagon  ta Najeriya ta fasa tafiya yajin aiki

Kungiyar Kwadagon Najeriya  wato NLC da gamayyar kungiyoyin kwadago ta TUC, sun janye yajin aikin gama-gari da suka shirya shiga a  yau Litinin, 28 ga watan Satumban 2020, bisa dalilin  karin farashin man fetur da wutar lantarki da aka yi a kawanaki baya- baya nan.

Karamin ministan  kwadago da samar da aikin yi  yace, an  cimma yarjejeniya ne sakamakon wani taro da gwamnati da wakilan kungiyar kwadago suka gudanar, wanda ya dauki tsawon lokaci har zuwa karfe uku saura, na daren ranar Lahadi .

Kungiyar kwadagon ta amince da janye yajin aiki  da ta shirya yi don matsawa gwamnati,  ta dawo da tallafin man fetur ta kuma rage farashin wutar lantarki.

Za a dakatar da sabon farashin man fetur na tsawon makonni biyu.

Minista Festus Keyamo, ne zai jagorancin kwamitin na masana da zai yi nazari a kan fito da sabon farashin kudin wutar lantarki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More