Karon farko cikin shekaru 15 Real Madrid ta sha kashi a Bernabeu a hannun Real Socied

Real Sociedad ta doke Real Madrid har gida da ci 2-0 a gasar Laliga mako na 18.

Dakika 3 da take wasa Willian José ya sa Sociedad a gaba da bugun fenareti bayan da aka busa ketar da Casemiro ya yi wa Mikel Merino.

Abubuwa sun sake dagulewa Real Madrid bayan da aka bawa Lucas Vasquez jan katin kora daga wasa a minti na 61.

Dakika 7 ya rage lokacin tashi wasa ya yi, Pardo ya sake jefa kwallo a ragar Real Madrid.

An tashi wasa Real Madrid 0-2 Real Sociedad

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Getafe 1-2 Barcelona

Sevilla 1-1 Atletico Madrid

Eibar 0-0 Villarreal

Bayan buga wasannin na mako 18, Barcelona ce ke ci gaba da darewa akan tebur da maki 40, Atletico Madrid na biye mata da maki 35, Sevilla na mataki name 3 da maki 33, Alves ta 4 da maki 31, sai Madrid ta 5 da maki 30.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More