Kasashen Denmark, Norwan da Iceland sun dakatar da allurar AstraZeneca bayan samun rahoton daskarewar jini

Kasashen Denmark, Norway da Iceland a ranar Alhamis sun a dakatar da amfani da allurar rigakafin Covid19 ta AstraZeneca kan damuwar da ake yi game da daskarewar jini bayan an yi wa mutum allurar, yayin da kamfanin da da ya samar da allurar rigakafin da masu kula da magunguna na Turai suka dage cewa allurar ba ta da wata illa.
Kasar Denmark ce ta fara sanar da dakatarwar, “bayan rahotanni masu tsanani na daskarewar jini” tsakanin mutanen da suka karbi allurar, a cewar Hukumar Lafiya ta kasar.
Hukumar ta jaddada cewa an dau matakin ne don kariya, kuma “ba a tantance ba, a halin yanzu, cewa ko akwai alaka tsakanin allurar rigakafin da kuma daskarewar jini”.
Koyaya, hukumar mai kula da magunguna ta Nahiyar Turai ta faɗi yau alhamis cewa babu wata alama mafi haɗarin yawan daskarewar jini a cikin waɗanda aka yi wa allurar rigakafin cutar ta Covid – 19, bayan da Denmark, Norway da Iceland suka dakatar da amfani da allurar rigakafin ta AstraZeneca.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More