Kashe bakar-fata a Amurka: Magajin Minneapolis ya kori ‘yan sanda guda hudu daga aiki

Magajin birnin Minneapolis da ke Amurka ya kore ‘yan sanda hudu daga aiki wadanda ake zargi da sanadin mutuwar wani mutum bakar- fata bayan sun kama shi.

A hotunan bidiyon da ganau suka nada a ranar Litinin, an ji mutumin, wanda yake da kimanin shekara 40, yana ihu yana gaya wa daya daga cikin ‘yan sanda wanda ya danne shi da gwiwar kafarsa cewa “ba na iya numfashi.” Magajin birnin, Jacob Frey ya yi Allah-wadai da abin da ya faru wanda ya bayyana a matsayin babban kuskure, sannan ya ce kasancewar mutum bakar-fata a Amurka ba laifin kisa ba ne.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More